Ministan tsaron jamhuriyar Nijer Kalla Moutari ya bayyana a wata sanarwar cewa, wannan ne muhimmiyar nasarar da sojojin kasashen biyu suka samu a wannan yanki, kasar Nijer za ta ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci da muggan laifuffuka.
Bisa labaran da kafofin watsa labaru na kasar Nijer suka bayar, baya ga harbe 'yan ta'adda 15, sojojin kasashen biyu sun lalata motoci 21 tare da samun wasu makamai. Kuma babu wani soja daga kasashen biyu da ya mutu ko jin rauni a yayin artabun da suka yi da mayakan 'yan ta'addan.
Jihar Tillabéri tana yammacin kasar Nijer. A shekarun baya baya nan, ana samun yawan hare-haren kungiyar 'yan ta'adda a yankunan dake tsakanin yammacin kasar Nijer da kasar Mali da kasar Burkina Faso, wadanda suka haddasa mutuwa da raunata mutane da dama. A ranar 1 ga watan Disamba, an kai hari kan wani gidan 'yan sanda dake jihar, wanda ya haddasa mutuwar mutum guda. (Zainab)