in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar EFCC ta Nijeriya ta musanta tsare 'ya'yan tsohon mataimakin shugaban kasar
2018-12-11 09:59:36 cri
Hukumar EFCC ta Nijeriya, mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tu'annuti, ta musanta tsare 'ya'yan tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, wanda kuma shi ne dan takarar shugaban kasar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakakin hukumar Tony Orilade, ya ce sun samu kiran waya da dama da sakonnin e-mail dake neman tabbacin ko sun tsare 'ya'yan Atiku Abubakar kamar yadda ake zargi, inda ma wasu ke cewa sun kai samame gidan ne domin neman takardun kudaden ketare.

Sai dai Ministan yada labarai na kasar Lai Mohammed, ya ce bangaren adawar na shirya labarai na bogi game da gwamnatin shugaban Kasar Muhammadu Buhari gabanin zaben 2019.

Ministan ya ce tun daga shekarar 2017, gwamnatin ke bayyana damuwa game da yada labaran bogi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China