in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun hallaka sojojin Najeriya 13 da 'yan sanda 2
2018-12-26 20:13:21 cri
Mahukuntan Najeriya sun tabbatar da rasuwar sojojin kasar 13 da 'yan sanda 2, sakamakon wani harin kwantan bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi musu, a kan hanyar Damaturun jihar Yobe, zuwa Maiduguri fadar mulkin jihar Borno.

Wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafin ta, ta rawaito rundunar sojojin kasar na cewa, maharan sun farwa jami'an tsaron ne a daren ranar Litinin.

Wannan hari dai ya biyo bayan wani harin da mayakan kungiyar suka kaiwa sansanin sojojin kasar dake Kukareta na birnin Damaturun jihar Yobe, jihar dake arewa maso gabashin kasar, wanda shi ma ya auku a ranar ta Litinin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China