in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kaddamar da jadawalin aikin bunkasa karkara na shekarar 2019
2018-12-29 20:55:04 cri
A ranar 28 da 29 ga watan nan na Disamba aka gudanar da babban taron kwamitin tsakiya mai kula da shirin raya karkara a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda aka tsara jadawalin aikin raya karkara da inganta aikin gona na shekarar 2019.

A lokacin taron, an gabatar da muhimman bayanai game da irin dabarun da za'a yi amfani dasu wajen aiwatar da shirin raya yankunan karkarar kasar Sin, an kuma gabatar da muhimman batutuwan da suka shafi aikin gona, yankunan karkara da yadda za'a kyautata yanayin rayuwar mutanen karkarar nan da shekaru biyu masu zuwa, kana an tsara jadawalin shirin raya karkara da aikin gona na shekarar 2019, kamar yadda kwamitin tsakiya mai kula da aikin raya karkara ya sanar.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kana shugaban kwamitin rundunar sojojin kasar Sin, ya gabatar da muhimmin bayani wanda ke shafar batun aikin gona, raya karkara da kuma rayuwar mazauna karkarar.

Shekarar 2019, wata muhimmiyar shekara ce dangane da manufofin gwamnatin Sin na neman cimma nasarar samar da al'umma mai matsakaiciyar wadata da kyakkyawar makoma daga dukkan fannoni. Yin aiki tukuru a fannin raya aikin gona, yankunan karkara da rayuwar mazauna karkarar zai bada gagarumar gudunmowa wajen tunkarar dukkan wasu kalubaloli da barazanar da ake fuskanta, kana zai tabbatar da samun nasarar raya tattalin arziki da kyautata yayanin zaman rayuwar al'umma, inji Xi. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China