in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da takarda game da zamanantar da aikin gona
2018-01-30 08:58:31 cri

Ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wasu ka'idoji game da yadda za a bunkasa yankunan masana'antun aikin gona na gwaji, a wani mataki na zamanantar da aikin gona a kasar.

Mataimakin ministan kimiyya da fasahar kere-kere na kasar Sin Xu Nanping wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya Litinin, ya ce makomar sashen noman kasar ta dogara ne ga yadda aka zamanantar da aikin gonan kansa, kuma hanya daya ta cimma wannan buri, ta ta'allaka ga yadda aka bunkasa fasahar kere-kere.

Xu ya ce, akwai bukatar a samar da karin kwarrru a yankunan gwajin da ake fatan kafawa, da kayayyakin aiki na zamani da kamfanonin dake samar da kayayyakln noma na zamani, ta yadda za a karfafa gasa a tsakanin bangaren aikin gonan kasar a cikin gida da kuma ketare.

Takardar ta bayyana cewa, nan da shekarar 2025, kasar Sin na fatan kafa yankunan masana'antun aikin gona na gwaji, bunkasa kirkire-kirkire a fannin aikin noma, kara samar da abinci, inganta bangaren kwadago da kara raya yankunan gwaji ba tare da gurbata muhalli ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China