A sanarwar da aka fitar bayan kammala zaman majalisar kolin kasar Sin wanda firaiministan kasar Li Keqiang ya jagoranta a jiya Laraba ta bayyana cewa, gwamnatin tsakiya za ta kara zuba kudi kimanin yuan biliyan 13, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2 wajen samar da tallafi da koyar da ilmin sana'a a yankunan tsakiya da yammacin kasar Sin, wadanda suka fi fama da talauci.
Kasar Sin za ta karfafa bangaren kudadenta, da inshora, da kuma tallafawa bangaren kamfanonin samar da madara.
Majalisar kolin ta kasar Sin ta ce tana bukatar yin amfani da yankuna 17 a matsayin na gwaji ciki har da birnin Beijing, domin zurfafa shirinta na bunkasa ci gaban fasahohi da ayyukan bada hidima. (Ahmad Fagam)