in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kaddamar da shirin tantance ingancin abinci a yankunan karkararta
2018-12-16 15:25:17 cri
Hukumomin kasar Sin, ciki har da ma'aikatar aikin gona da kyautata yankunan karkara sun kaddamar da shirin gangamin binciko nau'ikan kayan abinci marasa inganci a yankunan karkara a duk fadin kasar.

Manufar gudanar da shirin shi ne domin kokarin kakkabe munanan laifuka guda 6 gabanin shigowar sabuwar kalandar gargajiya ta al'ummar Sinawa, wadda za ta fado a ranar 5 ga watan Fabrairun shekarar 2019.

Hukumomin tabbatar da bin doka da oda na kasar za su mayar da hankali ne ga nau'ikan abincin da aka sarrafa su tare da alkinta su, da nau'ikan abincin taba ka lashe, da barasa, da kayan dandanon abinci da kuma madarar shanu da nau'ikan nama, wadanda galibi aka fi amfani da su a yankunan karkara, bayan da aka samu bayanai dake nuna cewa ana samun yawaitar kayayyakin abinci na jabu da kuma marasa inganci a yankunan karkara kuma ajandar wannan gangami za ta mayar da hankali ne kan wadannan nau'ikan kayan abinci.

"Ba za mu taba kawar da kai ba wajen binciko dukkan kamfanoni da masana'antun dake samar da irin wadannan haramtattun kayan abinci," in ji Han Changfu, ministan aikin gona da raya karkara na kasar Sin. "Dukkan wadanda aka same su da hannu wajen aikata makamanta wadannan laifuka za'a haramta musu gudanar da ayyukansu kana za'a tusa keyarsu zuwa hukumomin 'yan sanda idan akwai bukatar yin hakan," in ji ministan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China