A yayin taron manema labarai da ofishin watsa labarai na gwamnatin kasar Sin ya kira a yau Litinin, mataimakin ministan harkokin kimiyya da fasaha na kasar Sin Xu Nanping ya bayyana cewa, takardar da gwamnatin kasar Sin ta fitar, ta tabbatar da babban aiki dake gaban gwamnati, wato kafa yankunan ayyukan gona masu amfani da fasahohin zamani. Haka kuma, wadannan ayyuka sun hada da, kafa wasu kamfanonin ayyukan gona masu amfani da fasahohin zamani, karfafa ayyukan nazari game da fasahohin zamani, ba da horo ga manoma, kyautata tsarin gudanar da ayyukan gona, da kuma karfafa musayar ra'ayoyi kan wannan fanni da dai sauransu, ta yadda za a raya ayyukan gona ta hanyoyin zamani. (Maryam)