Sharhin ya yi bayani kan aniyar shugaba Xi Jinping ta inganta yunkurin yin kwaskwarima a cikin gida. Ya kuma ruwaito bayanan wasu jami'an sa ido a fannin kudi da jami'ai na kasashen ketare, don nuna yabo ga ma'anar manufar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare da Sin ta gudanar a cikin shekaru 40 da suka gabata, da kuma mihimmiyar rawar da Sin ke takawa wajen ciyar da tattalin arzikin duniya gaba yadda ya kamata, da kiyaye zaman karko na tsarin harkokin duniya da dai sauransu. A sa'i guda kuma, sharhin na cike da fatan alheri na ganin nasarorin da kasar Sin ta samu wajen gudanar da manufar za su amfanawa duk duniya, tare kuma da kafa makoma mai kyau ta hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa wajen neman ci gaban tattalin arziki a nan gaba. (Bilkisu)