in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun jinjinawa ci gaban Sin cikin shekaru 40
2018-12-19 13:17:19 cri

Masana da kwararru a fannin tattalin arziki, sun jinjinawa irin ci gaban da kasar Sin ta samu, a gabar da kasar ke cika shekaru 40 da fara aiwatar da gyare gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. Da yawa daga masu fashin baki dai sun bayyana nasarorin da kasar ta samu a matsayin wani abun ban al'ajabi.

Sin ta yi bikin cika shekaru 40 da fara aiwatar da wadannan manufofi a daukacin sassan kasar a jiya Talata.

Game da hakan, masani dake jagorantar wata cibiyar nazari dake Amurka Robert Lawrence Kuhn, ya ce, kasar Sin ta fuskanci turba mai bullewa, wato tsarin gurguzu mai halayyar musamman na kasa, kuma karkashin jagoracin JKS, mahukuntan ta sun sanya ci gaban al'ummar kasar, da ingantar rayuwar su sama da komai.

A nasa tsokacin, William Jones, na "Washington bureau" mai nazarin harkokin gudanarwa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Sin ta sauya matsayin yankunan ta daga masu fama da talauci zuwa yankuna mafiya daraja, da karfin tattalin arziki a duniyar yanzu.

Shi ma Farooq Sobhan, shugaban cibiyar "Bangladesh Enterprise Institute" cewa ya yi, hukumar samar da ci gaba ta kasa da kasa ta Sin, da hadin gwiwar bankin raya Asiya, da asusun raya sabuwar hanyar Siliki, sun shaida kudurin kasar na bunkasawa, da goyon bayan ci gaban tattalin arzikin yankin da kasar ta Sin take, da ma sauran sassan duniya baki daya.

Mr. Sobhan ya ce, wadannan matakai sun amfani kasar Bangladesh, da ma sauran kasashe masu tasowa, wajen samar da ci gaba, da fadada samar da ababen more rayuwar al'umma.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China