Baki daya an bayar da lambobin yabon ikon mallakar fasaha guda 40, wadanda suka hada da masu kirkire kirkire na fasahohin zamani masu matukar amfani guda 30, da kuma masu fasahar zane na masana'antu guda 10, inda suka lashe lambobin yabo na zinare.
Ya zuwa karshen shekarar 2017, kayayyaki da ayyukan da suka shafi wadanda suka karbi lambobin yabon na zirane 40 sun samar da kudaden shiga da ya kai yuan biliyan 83.5 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 12), sai ribar yuan biliyan 13.9 da kuma yuan biliyan 18.6 na kayayyakin da aka fitar zuwa ketare.
Sama da masu fasaha 60 ne suka samu lambar yabo ta azurfa, wadanda aka shigar da su a wannan shirin a karon farko domin bada kwarin gwiwa ga masu fasahar kirkire kirkire.
Shen Changyu, shugaban hukumar ikon mallakar fasaha NIPA, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan wadanda suka yi fice a fannin kirkire kirkiren fasahohin zamani.
Ba da lambar yabon na fasahar kirkire kirkire na kasar Sin na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar NIPA da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa. Sama da masu fasahar kirkire kirkire 6,000 ne aka karrama da lambobin yabo tun farkon bullo da shirin bada lambar yabon a shekarar 1989. (Ahmad Fagam)