Manazarta sun nuna cewa, kotun jama'a ta koli ta kafa wannan kotun mallakar fasaha, da kuma daukar nauyin sake yin shari'a kan wasu batutuwan laifi na keta hakkin mallakar fasaha, wannan ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin kyautata tsarin yanke hukunci kan batun laifi na mallakar fasaha, da nufin ingantawa da kiyaye ayyukan yin kirkire-kirkire kan kimiyya da fasaha. Kana ya kara nunawa kasashen duniya aniyar kasar da karfin da ta nuna wajen kara kiyaye mallakar fasaha. (Bilkisu)