Wang Yi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi, a gaban mambobin wata majalissar masana, game da harkokin da suka shafi kasa da kasa dake da ofishi a birnin New York.
Ya ce Sin da Amurka na gab da bikin cika shekaru 40, na kafuwar dangantakar diflomasiyya dake tsakanin su, don haka ya wajaba su nazarci sauye sauye da suka wakana ga juna, su zaburar da dangantakar su, tare da fuskantar inda suka dosa a fannin ci gaba.
Wang Yi ya kara da cewa, Sin ba za ta bi hanyar danniya da kasashe masu karfi suka bi a baya ba. Maimakon haka za ta nacewa hanyar gargajiya mai halayyar musamman, kuma Sin ba za ta yi kokarin kasancewar tamkar Amurka, ko ta kalubalance ta, ko ta yi yunkurin maye gurbin Amurkar ba.(Saminu Alhassan)