A gun taron, an zartas da sanarwar Santiago, da shirin ayyukan hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka da yankin Caribbean kan manyan fannoni tun daga shekarar 2019 zuwa 2021. Kana an zartas da sanarwar musamman kan shawarar "ziri daya da hanya daya". Bayan taron, Wang Yi da ministan harkokin wajen kasar Chile da na Salvador sun gana da 'yan jarida tare.
A gun taron, daya bayan daya Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen kasashen Chile, Cuba, Peru, Mexico, Venezuela, da sauran kasashen dandalin tattaunawar, kana sun gana da ministocin harkokin wajen kasashen yankin Caribbean 9 wadanda suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar Sin, tare da shugabannin kungiyoyin yankin Latin Amurka. (Zainab)