in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya jaddada goyon baya ga kudurorin ci gaba na hadin gwiwar kasa da kasa
2018-09-29 15:47:18 cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kasarsa na goyon bayan gudanar da harkoki tare tsakanin sassa daban daban, da wanzar da zaman lafiya, da kuma gudanar da cinikayya ba tare da sanya shinge ba. Wang Yi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar, yayin taron mahawarar da ta gudana jiya Juma'a a zauren MDD.

Ya ce kudurorin ci gaba na zamani da suka haifar da kafa MDD, sun tanaji bukatar kafa ka'idojin MDD, masu tallafawa tunani, da aiwatar da matakan gudanar da harkoki tare tsakanin sassa daban daban.

Ministan ya kara da cewa, tun tuni Sin ke martaba wannan manufa ta kasa da kasa, wadda jigo ce ga yunkurin da ake yi na samar da ci gaba cikin lumana, kuma za ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya, wajen ba da gudummawa ga tsaro, da zaman lafiyar duniya baki daya.

Ya kara da cewa, ci gaba ga ko wace kasa muhimmin batu ne, wanda ya dace a aiwatar bisa matsayin daidaikun kasashen, kuma Sin za ta nacewa bin tafarkin warware sabani ta hanyar bin doka, da tattaunawa, da shawarwari bisa daidaito, kuma ba za ta saduda, saboda matsin lamba daga wani sashe ba.

Daga nan sai minista Wang Yi ya bayyana matsayin Sin, game da tsayawa tsayin daka, wajen goyon bayan cinikayya maras shinge, da aiwatar da dokokin kasa da kasa, ta yadda za su amfani ko wane bangare, su farfado da tattalin arzikin duniya, don cimma moriya ga dukkanin kasashe.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China