An gabatar da daftarin dokar ne a wajen taron zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, don wakilan jama'ar kasar su tantance shi a karon farko.
Cikin daftarin dokar, an bukaci samar da goyon baya ga aikin nazarin allurar rigakafi, da masu neman gudanar da irin wannan nazari. Ban da haka kuma, ana kallon ayyukan nazari, da samar da allurar rigakafi, gami da ajiyarsu a matsayin manyan ayyuka masu matukar muhimmanci na kasar.
Haka zalika, daftarin dokar ya gabatar da karin wasu sharudan da ya kamata a cimma kafin a samu damar samar da alluran rigakafin, da kuma sayar da su. (Bello Wang)