in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin za ta kara goyon bayan kamfanoni masu zaman kansu
2018-12-22 16:19:56 cri
Yayin taro kan batun tattalin arziki na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka yi a jiya Jumma'a, an bayyana cewa, ya kamata a ba da taimako domin raya kamfanoni masu zaman kansu, da samar musu yanayi mai kyau bisa dokokin kasar, domin kiyaye tsaro na shugabannin kamfanonin da na iyalansu, da kuma tabbatar da tsaron dukiyarsu.

Kamfanoni masu zaman kansu sun ba da babbar gudummawa wajen raya kasar Sin, a shekarar bana, an fitar da manufofi da dama domin kwantar da hankulan shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, kaman daidaita yanayin kasuwannci, rage kudaden da kamfanonin suka kashe wajen gudanar da ayyukansu, da kuma kiyaye ikonsu yadda ya kamata da dai sauransu.

Mataimakin shehun malamin kwalejin koyon ilmin gudanar da harkoki na Guanghua na jami'ar Peking Yan Se ya bayyana cewa, a taron na wannan karo, kwamitin tsakiyar jam'iyyar JKS ta Sin ya kara yin bayani kan wasu harkokin dake janyo hankulan kamfanoni masu zaman kansu, kamar yadda za a kiyaye tsaro na shugabannin kamfanonin da kuma dukiyarsu, ta yadda za a warware matsalar samun jari da dai sauransu, lamarin da zai kara imanin kamfanoni masu zaman kansu.

A yayin taron, an kuma bayyana cewa, a fannin wannan manufar za a ci gaba da rage harajin kamfanonin. A fannin manufar kudade kuma, za a bada taimako ga kamfanoni masu zaman kansu da kuma kanana da matsakaitan kamfanoni wajen neman jari. A fannin manufofi kuma, za a samar da yanayi na adalci domin sa kaimi ga kanana da matsakaitan kamfanoni wajen neman bunkasuwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China