An ce tsunami ya abuku ne a daren ranar Asabar bisa agogon birnin Jakarta, bayan wani dutse mai suna Anak Krakatau ya yi amon wuta, lamarin da ya haddasa zabtarewar kasa a karkashin ruwan teku, da karuwar ruwan teku, in ji hulumar tinkarar bala'i ta kasar Indonesia.
Tsunamin ya rushe gidaje 556, da hotel 9, gami da jiragen ruwa 360, a yankin Pandeglang, inda aka samu hasara mafi tsanani, gami da sauran wasu yankuna 2, in ji Sutopo Nugroho, kakakin hukuma mai kula da aikin tinkarar bala'i ta kasar Indonesia. (Bello Wang)