in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 168 sun halaka a sakamakon tsunami a kasar Indonesia
2018-12-23 16:43:27 cri
A labarin da hukumar yaki da bala'u daga indallahi ta bayar a yau Lahadi, an ce, yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon igiyar ruwa mai karfin gaske da ake kira tsunami ya karu zuwa 168.

Kakakin hukumar, Sutopo Purwo Nugrohoya ya kara da cewa, bala'in ya kuma halaka gidajen al'umma da otel da kuma jiragen ruwa masu yawa.

A jiya da dare, babbar igiyar ruwa ta tsunami ta afkawa mashigin teku na Sund dake yammacin kasar Indonesia, sai dai ba a gano aukuwar girgizar kasa ba a lokacin. Ana shakku ko zabtarewar tsaunuka a karkashin teku a sanadin dutsen Krakatau da ya yi aman wuta da kuma cikar ruwan teku a sanadin cikar wata ne suka haddasa tsunami din. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China