in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 102 sun rasu sakamakon girgizar kasa a Indonesia
2016-12-09 11:17:20 cri
Bisa labarin da aka samu daga hukumar kula da harkokin bala'un kasar Indonesia, an ce, ya zuwa yanzu, mutane 102 suka rasu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.5 wadda ta auku a yankin musamman na Aceh dake lardin Sumatra na kasar, kana, ya zuwa yanzu, akwai mutum guda da ba a san inda yake ba, yayin da mutane 136 suka samu raukuma masu tsanani, kana mutane 616 sun samu kananan raunuka. Haka zalika, a halin yanzu kimanin mazauna yankin 3276 ne suka rasa muhallinsu sakamakon bala'in, kuma suna zaune ne a wani wurin da aka kebe musu, bugu da kari, shugaban kasar Joko Widodo ya ziyarci wurin da girgizar kasar ta auku domin jajantawa wadanda bala'in ya shafa. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China