in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin zai wuce dalar Amurka biliyan dubu 2 a shekarar 2018
2018-12-23 15:54:40 cri
A jiya Asabar 22 ga wata, Mr. Song Xianmao, mataimakin direktan hukumar kula da cinikin waje ta ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, yanayin cinikin waje da kasar Sin take ciki a shekarar 2018 yana da kyau, an yi hasashen cewa, yawan kayayyakin da aka shigo dasu kasar Sin zai wuce na dalar Amurka biliyan dubu 2, wato zai kai wani matsayin da ba a taba gani ba a tarihin kasar.

Mr. Song Xianmao ya bayyana cewa, tun daga watan Janairu zuwa watan Nuwamban bana, yawan kayayyakin da aka yi shigi da ficinsu a kasar Sin zai kai dalar Amurka biliyan dubu 4.24, wato zai karu da 14.8% bisa na shekarar 2017. Daga cikinsu, yawan kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan dubu 1.91, wato ya karu da 18.4% bisa na shekarar bara. Sakamakon haka, an yi hasashen cewa, wannan adadi zai wuce dalar Amurka biliyan dubu 2. Mr. Song Xianmao ya nanata cewa, dalilin da ya sa aka samu wannan kyakkyawan sakamako shi ne saboda kasar Sin ta aiwatar da manufar shigo da karin kayayyaki daga sauran yankunan duniya.

Mr. Song ya nuna cewa, a shekara mai kamawa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufar rage harajin kwastam da ake bugawa kan kayayyakin da ake shigo da su daga ketare, sannan za ta kara kyautata aikin kwastam ga kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China