in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na samun nasara a kokarinta na gudanar da ayyukan adana ruwa
2018-12-10 10:44:23 cri
Kasar Sin ta samu nasara a fannin gudanar da manyan ayyukan adana ruwa, yayin da take tsaka da kokarin inganta karfinta na takaita ambaliya da saukaka fari tare da samar da wadatuwar abinci da kyautata muhallin halittu.

A cewar Wang Annan, jami'i a ma'aikatar albarkatun ruwa na kasar, tun daga shekarar 2014 ake aiwatar da wasu ayyukan adana ruwa 132, inda suka lakume fiye da yuan triliyan 1, kwatankwacin dala biliyan 146.

Ya ce wadannan ayyukan sun inganta samar da ci gaba a cikin yankuna da kuma aikin kawar da talauci, la'akari da yadda kaso 75 na ayyukan 132 suka kasance a yankunan tsakiya da yammacin kasar, yayin da kaso 56 suka kasance a wuraren dake fama da talauci.

Ayyukan na daga cikin shirin kasar da aka sanar a shekarar 2014, da nufin gina wuraren adana ruwa 172 ya zuwa shekarar 2020.

Tuni sama a kaso 80 na ayyukan 172 za su fara gudana ya zuwa karshen 2019, kuma babban aiki irin wannan da za a yi a 2019 shi ne na yankin kogin Pearl. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China