in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin na cikin yanayin da ya dace
2018-12-14 19:48:49 cri

Yayin da shekarar 2018 ke shirin ban kwana, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da bunkasa yadda ya kamata, duk da matsin lambar da ya ke fuskanta, kana ya cimma ma'aunin bunkasar da ake fatan samu a wannan shekara.

A yau ne hukumar kididdigar kasar Sin (NBS) ta fitar da wasu alkaluman bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wadanda ke nuna irin ci gaban da aka samu a bangaren zuba jari, da daidaituwar kudaden da jama'a ke kashewa da kayayyakin da masana'antu ke samarwa ba kamar yadda aka saba ba.

Da yake karin haske, kakakin hukumar Mao Shengyong ya ce alkaluman da hukumar ta fitar, suna nuna karin nasara kan tattalin arzikin kasar Sin, wanda ke turba mai inganci.

Wannan ci gaba na nuna cewa, babu shakka kasar Sin za ta cimma burin da take fatan samu game da ci gaban tattalin arzikin na kusan kaso 6.5 cikin 100, kana tattalin arzikin zai samu tushe mai kyau a shekarar 2019 mai kamawa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China