in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage babban zaben Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo da sati guda
2018-12-21 10:39:48 cri
Kwamitin zabe mai zaman kansa na Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo ya sanar a jiya Alhamis cewa, za'a dage babban zaben kasar wanda da farko aka shirya yi a ranar 23 ga wata da tsawon mako guda, wato zuwa ranar 30 ga wata.

Shugaban kwamitin zaben, Corneille Nangaa Yobeluo ya bayyana a wajen taron manema labarai da aka yi a birnin Kinshasa cewa, har yanzu ba'a maye gurbin kayayyakin zaben da suka kone a kwanakin baya ba, wannan matsalar ta sa ba za'a iya gudanar da zaben cikin lokacin da aka tsara ba. Kana za'a jinkirta zaben 'yan majalisar dokokin kasar da na jihohi zuwa ranar 30 ga wata.

Corneille Nangaa ya ce, za'a kammala yakin neman zaben a yau Jumma'a kamar yadda aka tsara.

A ranar 13 ga wata, wani dakin adana kaya na hukumar zabe mai zaman kanta ta Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo dake Kinshasa ya kama da wuta, inda kayayyakin zaben masu tarin yawa suka kone, ciki har da injunan jefa kuri'a dubu takwas. Ana nan ana gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar, kuma a cewar gwamnatin kasar, akwai yiwuwar da gangan ne aka tayar da gobarar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China