in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya nuna damuwa game da abubuwan dake faruwa a DRC gabanin zaben kasar
2018-12-19 11:52:59 cri
Kwamitin sulhun MDD ya bayyana damuwa game da abubuwan dake wakana a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC kwanaki kadan gabanin gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan majalisu.

A wata sanarwar da aka rabawa manema labaru, mambobin kwamitin tsaron MDDr sun bukaci gwamnatin DRC da ta binciki abubuwan dake faruwa a kasar, inda wasu daga cikin abubuwan dake faruwa suna haddasa hasarar rayuka da barnata dukiyoyi.

Kwamitin ya bukaci dukkannin bangarorin kasar, gwamnati da bangaren 'yan adawa, dasu dauki matakan wanzar da zaman lafiya, a kokarin da ake na shirye shiryen gudanar da zaben kasar, domin tabbatar da samun zabe mai inganci, mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali a demokuradiyyar Kongon da kewayenta.

Mambobin MDD sun bukaci dukkannin bangarorin kasar dasu gujewa dukkan abubuwan da zasu iya haifar da tashin hankali na kowane iri, kuma su guji yin duk wasu kalamai na haifar da tunziri ko batanci wadanda zasu iya haddasa tashin hankali kuma su guji nuna banbance banbance dake tsakaninsu don samun kwanciyar hankali da lumana.

Zaben na ranar 23 ga watan Disamba ya kasance wata muhimmiyar dama irinta ta farko a fagen siyasar kasar, inda ake fatan sauya shugabanci cikin kwanciyar hankali da lumana, da tabbatar da zaman lafiya da samar da yanayi mai kyau don cigaban kasar, inji sanarwar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China