in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da bullar cutar Ebola guda 200 a DRC
2018-10-21 16:46:24 cri
Ma'aikatar lafiya ta jamhuriyar demokaradiyyar Kongo ta sanar a jiya Asabar cewa, an tabbatar da rahotan bullar cutar zazzabin Ebola kimanin 200 a yankunan gabashin kasar ta DRC tun daga watan Augastan wannan shekara.

A cewar alkaluman kididdiga na baya bayan nan wanda ma'aikatar lafiyar kasar ta wallafa, an samu rahotannin bullar cutar kimanin 200 a yankin Beni da kewaye dake lardin Kivu ta arewa, kuma daga cikinsu, mutane 117 cutar ta hallaka, yayin da mutane 61 da suka kamu da cutar sun riga sun warke.

Bayan taron tattaunawa da aka gudanar a Geneva, hukumar ta WHO ta sanar da cewa, a halin yanzu, cutar Ebola a DRC bata cikin yanayi na mummunar barazana dake bukatar daukin gaggawa daga kasa da kasa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China