in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD ya nanata bukatar samar da tsaro a yankin manyan tafkuna
2018-10-12 10:52:44 cri
Manzon musamman na MDD mai kula da yankin manyan tafkuna Said Djinnit, ya nanata bukatar kawar da dakarun kungiyoyi masu kokarin mayar da hannu agogon baya a yankin, a wani mataki na kokarin da ake yi na ganin al'amura sun inganta a Jamhuriyar demokuradiyar Congo(DRC)

Djinnit wanda ya bayyana hakan yayin zaman kwamitin sulhu na MDD game da halin da kasar ke ciki, ya ce matsalar tsaro a gabashin jamhuriyar demokiradiyar Congo na karuwar sakamakon ci gaba da kasancewar dakarun irin wadannan kungiyoyi.

Ya ce, baya ga haifar da matsalar tsaro da raba mutane da muhallansu, ayyukan irin wadannan dakaru na kara rura wutar rashin yarda tsakanin kasashen dake yankin, lamarin da ke kara haifar da barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China