in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Sudan ta amince da daftarin kudurin zama mamaban bankin AIIB
2018-12-12 09:44:31 cri
Majalisar dokokin kasar Sudan, ta amince da daftarin kudurin kasacewar kasar mamban bankin zuba jari domin samar da ababen more rayuwa na Asiya wato AIIB.

Majalisar ta amince da rahoton kwamitinta kan harkokin kudi da tattalin arziki wanda shugaban kwamitin Ali Mahmoud Abdul-Rasoul ya gabatar yayin zamanta na jiya Talata, game da kudrin zama mamban bankin.

Ali Abdul-Rasoul ya yi bayanin cewa, yanzu kasashe mambobin bankin sun kai 57, baya ga wasu karin kasashe 30 da suka aike da bukatarsu ta shiga.

Ya kara da cewa, tun bayan kafuwarsa a 2014, bankin ya aiwatar da ayyuka 28 a kasashe 28 kan kudi dala biliyan 5.5.

Har iya yau, ya ce kudurin zama mamban bankin ya kunshi babuka 10 da maudu'ai 60, da suka yi nazarin alfanun da Sudan za ta samu idan ta zama mamban bankin, musammam ma ta fuskar kudaden biyan ayyukan more rayuwa.

Mambobin kwamitin sun yabawa daftarin kudurin, inda suka bayyana muhimmancin zaman Sudan mamba a bankin AIIB, suna masu yabawa kasar Sin bisa shirye-shiryenta na bunkasa zuba jari a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China