Wata sanarwa da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Sudan ta fitar, ta ce za a aiwatar da yarjejeniyar ne cikin matakai 3.
Bangarorin biyu sun kaddamar da matakin farko na yarjejeniyar da ya kunshi samar da injina da suka hadar da tractor da injinan girbi da na samar da ruwa da suka lakume dala miliyan 2.2.
Sanarwar ta ruwaito kwamishinan kula da 'yan hijira na Sudan, Hamad Al-Jizouli na cewa, abu mafi muhimmanci a wannan matakin shi ne, sake fara ayyukan noma da samar da wutar lantarki.
Ya ce a yanzu, jihar White Nile dake iyaka da Sudan ta Kudu, na dauke da 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu sama da 150,000 a sansanoni, sannan akwai wasu sama da 88,000 dake garuruwan dake kusa da jihar.
Wani rahoton MDD na baya-bayan nan ya nuna cewa, ya zuwa ranar 15 ga watan Oktoban bana, adadin 'yan gudun hiijirar Sudan ta Kudu dake Sudan, ya kai 762,900. (Fa'iza Mustapha)