#Gyare-gyare da bude kofa# Xi: Ya kamata kasar Sin ta kara ingantawa gami da kyautata shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar
Yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a cikin shekaru 40 da suka gabata sun shaida cewa, shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin shi ne tushen tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin. Tsayawa kan jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin shi ne ya fi gaban kome wanda ba za'a iya canjawa ba ko kadan. Ya kamata a kare mutuncin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da tsayawa haikan kan shugabancinta yayin da kasar Sin take kokarin yin kwaskwarima da neman bunkasuwa, da raya harkokin cikin gida da na kasashen waje, da bunkasa harkokin tsaron gida da tafiyar da mulkin kasa da soja da sauransu. Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi jam'iyyar kwaminis ta himmatu wajen inganta karfinta a fannonin tafiyar da harkokin mulki da shugabanci nagari, ta yadda za'a bi hanya madaidaiciya, wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. (Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku