Yau a nan birnin Beijing babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, kirkire-kirkire yana taka rawar da ta fi muhimmanci ne, yayin da ake yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, haka kuma ya dace a ci gaba da 'yantar da tunanin al'ummun kasar kamar yadda ake. Kana dole ne a ci gaba da nacewa ga tunanin Marx da Lenin, da tunanin marigayi Mao Zedong, da ra'ayin marigari Deng Xiaoping, da muhimmin tunani na wakilci a fannoni uku, wato wakilci bukatun bunkasuwar karfin aikin kawo albarka na zamani, da wakilcin manufar ci gaban al'adu, da kuma wakilcin babbar moriyar tarin jama'ar kasar, da ra'ayin raya kasa ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha, da jagorancin tunanin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki, da nacewa ga 'yantar da tunani, da martaba hakikanin yanayin da ake ciki. Ban da haka, ya kamata 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin su sauke nauyin raya tunanin Marxism dake wuyansu a karni na 21.(Jamila)