Yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yayin babban taron taya murnar cika shekaru 40 da kasar Sin ta fara aiwatar da munufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje cewa, kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin da kuma ingiza gyare-gyare da bude kofa da babban sha'anin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, manyan ayyuka uku ne na al'ummun kasar Sin tun bayan shekarar 1919, wadanda ke da babbar ma'ana a tarihi, yayin da ake kokarin farfado da al'ummun kasar ta Sin.(Jamila)