in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta rattaba hannu kan yarjejniyar dala miliyan 244 na ginin tituna da kamfanonin kasar Sin
2018-12-14 15:56:52 cri
Hukumar kula da tituna ta Habasha, ta rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi 4 da kamfanoni 4 na kasar Sin, domin ginin tituna da za su lakume dala miliyan 244.

Ana sa ran za a yi ginin titunan da tsawonsu baki daya ya kai kilomita 290.5 a sassan tsakiya da arewaci da gabashi da kuma yammacin kasar.

Kamfanonin hudu da za su yi aikin sun hada da kamfanin gine-gine na CCECC da Zhejiang Bayong Highway Engineering da kamfanin Hebei Construction Group Corporation da kuma Beijing Urban Construction Group. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China