in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Habasha ta tsare manyan jami'an soji 27 bisa zargin cin hanci
2018-11-13 11:40:09 cri
Atoney Janar na Habasha Berhanu Tsegaye, ya bayyana a jiya cewa, manyan hafsoshin sojin kasar 27 ne aka tsare cikin karshen makon da ya wuce, game da zargin cin hanci.

Yayin wani taron manema labarai a birnin Addis Ababa, Berhanu Tsegaye, ya ce an aiwatar da ayyukan cin hanci ne cikin shekaru 6, daga shekarar 2011 zuwa 2017, inda suka hada da sayen kayayyakin da darajarsu ta kai dala biliyan 2, ciki har da jirgin sama da na ruwa da injin daukar kayayyaki.

Ya kara da cewa, ana zargin kamfanin karafa da gine-gine na MeTec, dake da alaka da wani babban jami'in soji, wanda kuma ke gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa da dama, da aikata mafi yawan cin hancin.

Ya ce jami'an kamfanin da fararen hula dake da kusanci da su, na da hannu cikin sayen jiragen da wasu kayyakin ta haramtacciyar hanya, inda suka zura wani bangare na kudin cikin aljihunsu.

Har ila yau, ya ce an tsare wasu mutane 36, galibinsu jami'an leken asiri, wadanda ake zargi da take hakkokin bil adama da suka hada da gallazawa da kisa da fyade da sace mutane. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China