Bikin baje kolin na kasa da kasa na Habasha za'a gudanar da shi ne daga ranar 1 zuwa 5 ga wannan wata na Nuwamba, zai samu halartar kamfanonin cikin gida da na kasashen waje da suka hada da kasashen Sin, Girka, Rasha, India, Singapore, Masar, Saudi Arabia, Hadaddiyar daular larabawa, da kuma Iran, jami'in shirin daga majalisar ciniki da zuba jari ta kasar Habashan (ECCSA), shine ya tabbatar da hakan a jiya Laraba.
Kafanonin da zasu halarci bikin daga kasashen Afrika sun hada da Sudan, Somalia da Morocco da dai sauransu, zasu bi sahun mahalarta bikin na tsawon kwanki 5, wanda za'a baje kolin kayayyaki da masu aikin bada hidima zasu taru a Addis Ababa, babban birnin kasar, in ji jami'in na ECCSA.
Masu zuba jari daga kasashen waje zasu yi amfani da wannan dama wajen shiga kasuwannin kasar Habashan, inji sakatare janar na majalisar ECCSA, Endalkachew Sime.
Ya kara da cewa, bikin baje kolin wata babbar dama ce ga kasar ta gabashin Afrika wajen jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje zuwa kasar. (Ahmad)