in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano sinadarin dake yakar cutar Ebola a jikin bil adama
2018-12-14 11:25:16 cri
Masana sun gano wani sinadari mai gina jikin dan adam wanda ke taimakawa wajen yakar kwayoyin cutar Ebola mai saurin kamawa, kamar yadda wani rahoton binciken hadin gwiwa na jami'ar Northwestern Georgia, da jami'ar California, da ta San Francisco (UCSF) da kuma cibiyar Gladstone suka gudanar.

A cikin binciken, masanan sun yi amfani da wasu dabaru wadanda ake iya gano yadda sinadarin proteins mai gina jiki dake jikin bil adama yake yin mu'amala da sinadarin proteins dake cikin kwayar cutar Ebola. Masanan sun samu kwakkwarar shaida dake nuna yadda ake samun cudanya tsakanin sinadarin na jikin kwayar cutar Ebola wato VP30 da kuma sinadarin jikin dan adam na RBBP6.

"Idan har ka dauki wannan sinadarin da na kwayoyin halitta na jikin bil adama, zaka iya dakile kwayar cutar Ebola," in ji jagoran marubuta binciken Judd Hultquist, mataimakin farfesa a fannin ilmin likitanci a sashen nazarin kwayoyin cutuka na jami'ar Northwestern University a tsangayar kiwon lafiya. "Haka zalika, idan ka fitar da sinadarin RBBP6 daga jikin kwayoyin halittar dan adam, kwayar cutar Ebola zata iya yaduwa cikin sauri."

"Wannan muhimmiyar cudanya ce, "inji Nevan Krogan, babban marubucin binciken kana farfesa a fannin nazarin kwayoyin halitta na jami'ar hada magunguna ta UCSF. "Sai dai a cewarsa har yanzu akwai alamar tambaya game da ko za'a iya amfani da sakamakon binciken ta yadda zai iya yin tasiri wajen magance cutar ta Ebola. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China