in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: An samun nasara a aikin yaki da Ebola sai dai fa akwai sauran rina a kaba
2018-08-24 20:32:22 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce ana cimma manyan nasarori a yakin da ake yi da cutar Ebola mai saurin kisa yanzu haka a janhuriyar dimokaradiyyar Congo, ko da yake, mai yiwuwa a sake samun wani karin barkewar cutar ko da karo daya ne a nan gaba.

Hakan kuwa na da nasaba da yanayin muhalli mai sarkakiya dake da nasaba da halin tsaro da wuyar shiga wasu sassa.

A cewar mataimakin babban daraktan WHO mai lura da ayyukan shirye shiryen gaggawa Peter Salama, ya zuwa ranar Alhamis, yawan mutane da aka tattara alkaluman su, na kamuwa da cutar sun kai sama da 100, cikin su hadda 103 da aka tabbatar sun kamu, kana wasu 63 sun rasu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China