in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na ci gaba da damuwa game da yanayin rikicin Kamaru
2018-12-14 11:03:09 cri
Manzon musamman na MDD a yankin tsakiyar Afrika, Franscois Lounceny Fall, ya ce yana ci gaba da damuwa da yanayin da da ake ciki a yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru, yana mai jaddada kudurin MDD na martaba 'yanci da hadin kan kasar.

A watannin baya-bayan nan, rikici tsakanin 'yan aware da dakarun Kamaru ya tilastawa daruruwan mutane tserewa, yayin da wasu daruruwan suka rasa rayukansu a yankunan biyu dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi, a kasar da masu amfani da harshen Farasanci suka fi rinjaye.

Francois Fall, ya shaidawa Kwamitin Sulhu na MDD a jiya cewa, har yanzu ba a daina rikici ba, inda kuma dukkan bangarori ke zargin juna da take hakkokin bil adama.

Ya kuma waiwayi ziyarar da ya kai kasar a watan Nuwamba, inda ya gana da manyan jami'an gwamnati, tare da jaddadawa masu ruwa da tsaki bukatar tattaunawa da dukkan bangarori a matsayin hanya mai dorewa ta sulhunta rikicin.

A don haka, ya yi kira ga gwamnatin Kamaru ta ci gaba da ba jami'an agaji damar isa ga jama'ar dake bukatar taimako tare, da tabbatar da an magance da duk wata matsala ta take hakkokin bil adama. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China