in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Sin: Ba za a kyale yadda aka ci zarafin 'yan kasar Sin ba
2018-12-11 14:49:53 cri

Wang Yi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, ya furta a yau Talata, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin, cewa kasar Sin ba za ta taba nade hannunta ta bari a ci zarafin 'yan kasarta da ma keta hakkinsu ba.

Jami'in ya yi furucin ne yayin bikin bude taron karawa juna sani dangane da yanayin harkokin kasa da kasa da aikin diplomasiyya na kasar Sin a shekarar 2018. Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin a ko da yaushe tana mai da hankali kan kula da lafiyar duk wani dan kasarta dake ketare, kuma za ta yi iyakacin kokarinta wajen ganin ta kare hakkin jama'ar kasar Sin, gami da tabbatar da yi musu adalci a duniya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China