in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta aike da sammaci ga Jakadan kasar Canada domin nuna adawa da tsare babbar jami'ar kamfanin Huawei
2018-12-09 16:20:58 cri

Mataimakin Ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng, ya aike da sammaci cikin gaggawa ga Jakadan kasar Canada a Sin, John McCallum, domin mika korafi da nuna adawa da tsare wata babbar jami'ar kamfanin fasaha na Huawei Technologies Co. LTD da hukumomin Canada suka yi.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Sin ta fitar a jiya, ta ce tsare 'yar asalin kasar Sin a lokacin da ta ke sauya jirgi a Vancouver na Canada bisa bukatar Amurka, ya take halaltattun hakkoki da 'yancinta.

Sanarwar ta ce irin wannan yunkuri ya yi watsi da doka sannan abu ne mara ma'ana da bai dace ba kwata-kwata.

Le Yucheng, ya ce kasar Sin ta bukaci Canada ta gaggauta sakin Jami'ar tare da kare 'yanci da hakkokinta, ko kuma ta jira martanin da za a dauka kanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China