in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira ga dukkan bangarori su taimaka wajen gudnar da sahihin zabe a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
2018-12-14 10:21:21 cri
Biyo bayan gobarar da ta lalata kayayyakin zabe a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, MDD ta yi kira ga dukkan bangarori, da su taimaka wajen gudanar da sahihin zabe a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo cikin kwanaki 10 masu zuwa.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya ce Majaisar ta riga ta bayyana damuwarta, ta hannun shugabar shirinta na wanzar da zaman lafiya na MONUSCO dake kasar wato Leila Zerrougi, game da duk wani yunkuri daga bangarori daban-daban, na kawo cikas ga zaben, sannan kuma ta karfafawa dukkan bangarori gwiwar taimakawa wajen gudanar da sahihin zabe.

Da farkon makon nan ne aka fitar da rahotannin da ke cewa, rikici ya barke tsakanin wasu bangarorin a birnin Kinshasa.

Shirin MONUSCO, ya bayyana a jiya cewa, gobara ta tashi a gidan adana kayayyaki na hukumar zabe ta kasar mai zaman kanta dake birnin Kinshasa. Kuma rahotannin farko sun nuna cewa, kayayyakin zabe na tasoshin zabe dake birnin da kuma adadi mai yawa na na'urorin zabe da sauran wasu kayayyaki, sun lalace sanadin gobarar.

An shirya gudanar da zabe a kasar mai arzikin albarkatu, wadda kuma yaki ya daidaita, a ranar 23 ga watan nan na Decemba, domin zaben wanda zai maye gurbin shugaba Joseph Kabila da ya kasance kan karagar mulki tun a shekarar 2001, a lokacin da ya maye gurbin maihaifinsa Laurent Kabila da aka kashe. Joseph Kabila bai sake tsayawa takara ba saboda ya zarce wa'adinsa na mulki biyo bayan soke zabukan 2016. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China