in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: An samu sabon rahoton bullar cutar Ebola a DRC
2018-08-02 09:35:39 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar a jiya Laraba cewa jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC ta sanar da cewa an samu sabon rahoton bullar cutar Ebola a kasar, 'yan kwanaki kalilan bayan da aka ayyana cewa an kawo karshen annobar a yankin yammacin kasar mai nisa.

Gwamnatin DRC ta sanar a jiya Laraba cewa, sakamakon farko na binciken da aka gudanar a dakunan gwaje gwaje sun nuna cewa an gano kwayar cutar ta Ebola ne a arewacin lardin Kivu, wanda bai wuce mako guda ba bayan da ma'aikatar lafiyar kasar ta bada sanarwar cewa an kawo karshen annobar a lardin Equateur wanda ke yammacin kasar, tazarar lardin arewacin Kivun ya kai nisan kilomita 2500.

Hukumomin lafiya na kasar sun sanar da cewa 4 daga cikin gwaje gwaje 6 da cibiyar nazarin magunguna ta kasar INRB dake Kinshasa ta gudanar sun nuna cewa, an tabbatar da kwayoyin cutar ta Ebola. Ana cigaba da yin gwaje gwajen.

Arewacin Kivu ya karbi bakuncin 'yan gudun hijira sama da miliyan guda kana ya hada iyakoki da kasashen Rwanda da Uganda inda ake matukar samun zirga zirgar al'umma don gudanar da harkokin cinikayya. A halin yanzu hukumar WHO tana yin aiki tare da makwabtan kasashe domin tabbatar da ganin hukumomin kiwon lafiya suna zaune cikin shirin ko-ta-kwana. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China