in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakiliyar MDD: Matsalar tsaro na barazana ga zabukan DRC
2018-10-12 10:04:30 cri
Shugabar tawagar MDD dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jamhuriyar demokiradiyar Congo Leila Zerrougui ta yi gargadin cewa, matsalar tsaro na barazana ga zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar da za a gudanar a watan Disamban wannan shekara.

Da take yiwa kwamitin tsaron majalisar karin haske, jami'ar ta ce yayin da kasar ke shirin gudanar da zabukan na watan Disamba, karuwar matsalar tsaro da ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai a kasar na ci gaba da haifar da babban kalubale.

Ta ce muddin ana bukatar a gudanar da zabuka masu tsafta kuma cikin lumana, wajibi ne a tabbatar da tsaron 'yan takara, da samar da yanayin yakin neman zabe mai kyau da ma gudanar zabukan kansu. Sai dai ta ce, yana da wahala a samar da tsaro a yankunan da kungiyoyi masu dauke da makamai suka ja daga, inda suke kara kafewa da manufofinsu na siyasa domin biyan bukatunsu.

Jami'ar ta MDD ta ba da shawarar bullo da matakan tsaro na siyasa da ma inganta hukumomi da jami'an tsaron kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China