A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar, mambobin kwamitin sun mika sakon ta'aziya ga iyalan wadanda aka kashe ciki har da dakarun wanzar da zaman lafiya 7 daga kasar Malawi da guda daga Tanzaniya da kuma a kalla sojoji 12 'yan kasar ta DRC, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
A ranar Larabar da ta gabata ce dai aka kashe sojojin, yayin da suke kai hare-haren hadin gwiwa karkashin laimar MDD wato MONUSCO da sojojin Jamhuriyar demokiradiyar Congo a kan dakarun kungiyar 'yan tawayen ADF a DRC da Uganda da yankin Beni dake arewacin Kivu.
Mambobin kwamitin sulhun sun kuma bayyana goyon bayansu ga dakarun kasashen Malawi da Tanzaniya, wadanda ke ci gaba da aiki a yanayi mai wahalar gaske a kokarin da suke yi na kare mazauna wuraren daga hare-haren mayakan na ADF da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai.(Ibrahim)