in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen dake kan shawarar "ziri daya da hahya daya" suna kara zurfafa mu'amala da kasar Sin
2018-10-22 10:22:54 cri
Baki daya an cimma matsaya kan yarjejeniyar bunkasa ayyukan samar da kayayyaki na hadin gwiwa kimanin 65, wanda aka kiyasta kudin a kan RMB yuan biliyan 142.7 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 20.6), yarjejeniyar wadda aka rattaba hannu a taron dandalin kasa da kasa da aka kammala a lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin.

Sama da wakilai 2,500 daga kasashen duniya 94 ne suka halarci taron, mafi yawan kasashen da suka halarci taron suna kan hanyar shawarar "ziri daya da hanya daya", wadanda suka halarci taron kolin kasa da kasa da zummar bunkasa samar da kayayyaki da cinikayyar hadin gwiwa da aka gudanar a Wuhan, babban birnin lardin Hubei, tsakanin ranakun 19 zuwa 20 ga watan Oktoba.

Daga cikin wakilan, akwai jami'an gwamnatoci, da shugabannin 'yan kasuwa, da na kamfanoni daga kasashen waje wadanda ke kokarin janyo hankalin Sinawa masu zuba jari, da zurfafa mu'amala da kasar Sin wajen bunkasa samar da kayayyaki.

Admasu Nebebe, karamin ministan kudi da hadin gwiwar tattalin arziki na kasar Habasha, ya fada a lokacin taron dandalin cewa, masu zuba jari daga kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa wajen daga matsayin layin dogon kasar Habasha da kuma bunkasa kayayyakin more rayuwa a kasar, wanda hakan ya baiwa kasar damar yin takara a harkokin cinikayyar kasa da kasa.

Ya ce kasar Habasha ta samu damammakin aiwatar da wasu tsare tsaren dake janyo hankalin masu zuba jari daga ketare. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China