Wani rahoto da aka fitar a ranar Talata, ya nuna cewa yanayin karbar haraji a kasar Sin ya kara kyautata a shekarar 2017, ciki hadda lokacin tabbatar da shigar harajin, wanda a yanzu ya ragu da kusan sa'o'i 142, matakin dake nuna raguwar lokaci da kaso 31.4 bisa dari a duk shekara.
Rahoton na shekara wanda babban bankin duniya da cibiyar PwC Global suka fitar, ya nuna raguwar yanayin biyan harajin da maki bakwai, matakin da ya nuna kara ingantar yanayin bada hidima a fannin biyan harajin. (Saminu Hassan)