in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin ya bunkasa a Oktoba yadda ya kamata
2018-11-14 13:48:52 cri
Kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin Liu Aihua ta bayyana a yau cewa, alkaluman kididdigar tattalin arziki na watan Oktoba na nuna cewa, an kiyaye fannoni daban daban da raya tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata, ana da sharadin ci gaba da raya tattalin arzikin kasar.

Rahotanni na cewa, yawan kayayyakin masana'antu da aka samar a watan Oktoba ya karu da kashi 5.9 cikin dari bisa na makamacin lokacin bara, yawan sha'anin bada hidima ya karu da kashi 7.2 cikin dari, kana yawan jarin da aka zuba daga watan Janairu zuwa Oktoba ya karu da kashi 5.7 cikin dari. Ana kiyaye raya fannonin samar da kayayyaki da biyan bukatu, samar da aikin yi, da farashin kaya da sauransu yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China