Kasar Sin za ta fara amfani da sabbin layukan dogo guda 10 kafin karshen shekarar 2018
Rahotanni daga kasar Sin na cewa, za a fara amfani da sabbin layukan dogo guda 10 da tsayinsu ya kai kimanin kilomita 2,500 kafin karshen shekarar 2018 da muke ciki. Wannan mataki zai taimaka wajen inganta layukan dogo masu saurin tafiya na kasar.
Bayanai na nuna cewa, za kuma a fara amfani da jirage masu saurin tafiya guda 553 a daidai wannan lokaci, inda ake fatan hakan zai daga matsayin bangaren sufurin jiragen kasa na kasar ya zuwa kaso 9 cikin 100.(Ibrahim)