Bikin ya samu halartar wasu jami'an gwamnatin kasar ta Tanzania, da kungiyar masu sada zumunta da dalibai matasa dake kasar, wadanda yawansu ya wuce 200.
A jawabinsa yayin bikin ministan kula da harkokin sufuri na kasar Tanzania Leonard Chamuriho ya bayyana cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, hanyar dogo da ta ratsa Tanzania da Zambia ta taka muhimmiyar rawa wajen kara sada zumunta da hadin kai a tsakanin kasashen Sin, Tanzania da kuma Zambia, ta kuma taimaka ga ci gaban rayuwar al'umma da tattalin arzikin kasashen Tanzania da Zambia, a sa'i guda tana da muhimmanci kwarai ga ayyukan 'yantar da al'ummar kasashen dake kudancin Afirka. (Bilkisu)