in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara gina sabon layin dogo mai saurin tafiya a yankin gabashin kasar Sin
2018-01-17 09:06:43 cri

A jiya Talata ne aka fara aikin gina sabon layin dogo mai saurin tafiya a lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, a wani bangare na hade yankin arewaci da kudancin kasar dake bakin teku da layin dogo.

Ofishin kula da harkokin jiragen kasa na lardin Jiangsu ya bayyana cewa, layin dogon mai tsawon kilomita 157 zai hade biranen Yancheng da Nantong, kuma za a shafe shekaru hudu kafin a kammala aikin, za kuma a kashe tsabar kudi har Yuan biliyan 26, kwatankacin dalar Amurka biliyan 4 a kan wannan aiki.

Idan aikin ya kammala, lokacin da ake dauka na tafiya tsakanin biranen biyu zai ragu daga kimanin sa'o'i biyu zuwa mituna 40 kacal.

Mataimakin gwamnan lardin Jiangsu Lan Shaomin ya ce, layin dogon tsakanin Yancheng zuwa Nantong zai taimaka wajen bunkasa lardin Jiangsu da yankin dake mashigar teku ta kogin Yangtze wato lardunan Zhejiang da Jiangsu da kuma birnin Shanghai.

Lardin na Jiangsu dai yana daga cikin lardunan da suka fi ci gaba a kasar Sin, yayin da yankin dake mashigar teku ta kogin Yangtze ke zama daya daga cikin cibiyoyin tattalin arzikin kasar ta Sin, yankin da ya hade Shanghai da wasu sassa na lardunan Jiangsu da Zhejiang da kuma Anhui.

Ya zuwa karshen shekarar 2017, kasar Sin tana da layukan dogo masu saurin tafiya da suka kai tsawon kilomita 25,000, adadin da ya kai kaso 66 cikin 100 na layukan dogo na duniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China